*MU KOMA TSANGAYA*

Assalamu alaikum
Takaitacciyar  Fira kenan da aka gabatar Tare da
*Gwaninmu Al hafith Yahya Mhd Auwal*
Wanda ya gabatar:
Yusuf abdulkarim

Q1...Da Farko mallam zai gabatar
mana da chikyan kyan sunan sa da
adreshinsa ma ana inda yafito
sannan mallam yay mana bayanin
ranar hayhuwar sa mallam

Q2.....To alhmdllh mallam ko xaka
iya bamu Wache shekara kafara
saka ka a makarata Wache tsangaya
aka kaika
Answr....To Alhamdu Lillah Gaskiya
Ba Zan Iya Tina Lokacin Da Na Fara
Karatu Ba
Kawai Tãshi Nayi Naga Ina Karatu
Kasan Cewar Baba Na Mai Tsangaya
Ne
Amma Kuma Na Fara Fita Rani A Shekara Ta 2011

Q3.....To Alhmdllh ko xaka iya fada
mana wanna gari kafara zuwa raani
sannan bayan kaje raani kadawo ina
kakara fita bayan shekara da ta
xagayo ma ana xaka fada mana
adadin garuruwan da kaje kafafata
karatu sannan kafafa mana adadin
malaman da kaxauna a wajensu
suka koyar da kai
Answr....Eh Farko Fita Ta Garin
Gombe Na Fara Zuwa Kuma Da She
Kara Ta Dawo Ma Can Din Na Sake
Zuwa
Zuwan Farko Mun Zauna A
Tsangayar Gwani Musa A Unguwar
Fantami
Zuwa Na Biyu Kuma Mun Zaunane A
Tsangayar Goni Adam A Unguwar
Arawa,
To Daga Nan Ban Kara Zuwa Ko Ina
Kararuu ba Duk Abinda Na Yi Awajan
Mahaifi Na Nayi *Aramma Malam Lawan*

Q4........allahu Akbar to mugode
sosai da wannan amsoshin naaka
yan kunajin dai yanda hirar taamu
take kasan chewa da mallam yahaya
Muhammad auwal Tareda ni Yusuf
abdulkarim to mallam yahaya ko
xaka iya fada mana a Wache shekara
kafara sauka
Answr....Eh Na Fara Sauka Ne A Shekara Ta 2014

Q5.....ikon Allah da hadda ka sauka
kokuwa da tilawar ixu nawa kasan
mafi akasari ba kasafai mutum yake
sauka da tilawa ba sai Wanda Allah
yaxaba
Answr.....Alhamdu Lillahi Na Samu
Tilawa Tun A Sauka Ta Farko Sai Na
Kara Sauka Ta Biyu Lokacin Kuma
Tilawar Tayi Karfi Sosai Kawai Sai Na
Kama Satu.!
A takaice malam yasamu hadda
Yanada Shekara (18).

Q6......Tofa jama a kunji baywa da
Kuma tsan tsar ikon Allah mallam ko
xaka iya fada mana wanna qwalu
bale ka fuskanta yayinda kake
gwagwar Maya ta Neman Al kur ani
kasan harkar karatu akwai matsaloli
da suke riskar mutum kala kala
kamar
Rashin wajen kwana mai kyau
Rashin sutura
Rashin abinchi
Rashin kudi
Sannan xaka fada mana shin sauka
nawa kayi karubuta alkur Ani ko
baka rubuta ba
Sannan wanna abune Wanda baxaka
taba mantawa dashi a rayiwarka ba?
Answr.....To Alhamdu Lillah Na Samu
Kalu Bale Da Yawa Awajan Neman
Karatu
Amma Ni Ban Samu Wata Matsala Ta
Rashin Kudi Ba SBD Lokaci Bayan
Lokaci Mahaifi Na Yana Zuwa Gombe
In Kuma Yazo Zamu Hadu Da Shi
Kuma Zai Bani Kudi In Kai Gurin
Malami Na Ya Ajiye Min Duk Sanda
Na Bukata Sai In Karbo.
Amma Na Dan Samu Matsalar Gurin
Kwana A can Tsangayar Gwani Musa
Na Unguwar Fantami Lokacin Babu
Masauki Sosai Sai Aka Saka Mu
Acikin Wani Gareji Na Mota Anan
Muke Kwana Malam Gamu Da Yawa
Sosai Aciki Da Masu Fitsarin Kwance
Ko Mutum Ba Yayi Kawai Sai Ya
Tashi Yaji Wani Ya Masa.!
To Kafin Na Dawo Daga Rani Na Na
Karshe Ranar Da Zamu Dawo Gida
*Bojude* Munje Bara Mun Dawo *Is
Kali* Da Safe Bana Mantawa Akwai
Wani Rami A Kusa Da Iskalin Mu
Muna Cikin Iskalin Kawai Sai Wasu
Yara Suka Tsoka No Wani Mahaukaci
Sai Ya Biyo Su Da Gudu Su Kuma
Kawai Sai Suka Shi Go Cikin Iskalin
Mu Haba Sai Jama,a Suka Fara
Guduwa To Lokacin Ina Da Dan
Laruri Na Ciwan Qafa Bana Iya Gudu
Sosai Nima Sai Na Fara Gudu
Tsautsayi Yasa Naje Na Fada Cikin Wannan Ramin.! Kawai Sai Fito Dani Akai Na Karye
Akafa.
Sai Aka Dawo Dani Gida Wato
*Bojude* Akayi Jinyata Har Na
Warke Na Fara Tafiya Da Sanda Ashe
Aikin Bai Yi Kyauba An Yimin Gyara
Ya Kai Sau Uku Ba Adace Ba
Sai Mahaifi Na Yayanke Sha Warar
Za Akaini Kasar Waje Domin A Gyara
Min Kafata
Ikon Allah Kenan Kawai Ana Cikin Haka Sai Allah Yayiwa Mahaifi Na
Rasuwa.!!!
Har Yanzu Dai Maganar Da Nake
Maka Sai Na Dogara Sanda Nake
Tafiya.!
_Amma Na Godewa Allah Wannan
Jinyar Bata Hanani Karatuba_
*Acikin Wannan Larurin Na Hada
Tilawa Ta Har Nayi Satu Har Na
Rubuta Qur,ani Kuma Na Taba Wasu
Ban Garori Na Ilimi Kuma Tsangayar
Baba Na Yanzu Haka Nine Mai
Darasu, Alhamdu Lillah.

*Q7.....Mallam ko yanada aure ko
sai gaba ?
Answr.....Allah Sarki *Har Yanzu Bani
Da Aure*
Rayuwa Kenan Mahaifina Yayiwa
Wasu Da Dama Aure Ni Kuma Ni Zanwa Kaina.!

Q8......A takaice malam yanzu haka
kanada dalibai kamar sunkai nawa?
*Answr....Eh Ina Da Daliban Ilimi Da
Kuma Na Alqur,ani Da Dama.*
*Jama a kunji fa tarihin matashi Dan
shekara 23 Kuma haxikin fasihi
Mahaddachin kur ani Allah yakara
yawaita mana irin ku a doron kasa.👏

_Wassalamu Alaikum
warahmatullahi wabarakatuhu_

Mai Gabatarwa Yusuf Abdulkarim
*Wanda ya tattara*
*Nuraddeen Umar Al Husary (Autan Ƙolawa)