Shin ko kasan wanene Gwani Yahya Mhd Auwal Bojude, hazikin matashi dan baiwa da bai wuce shekara 24 ba, wanda Allah yai masa baiwar sanin Al'qur-ani da Logar sa.....

"Wallahi kullum zargin kaina nake; Allah ya bani dama sosai tayin karatu, zan fara aiki da ita sai ta kubuce min, ina Nufin Mahaifina ! da Allah yasa yana raye da nayi karatu sosai. 
Allah yai masa rahama 😭"- Gwani Yahya Bojude

An haifi Gwani Yahya a garin Bojude dake karamar hukumar kwami cikin jihar Gombe a shekarar 1996.

Ya fara karatun Al'qur-ani ne tun yana dan kankani a wajen mahaifinsa Alaramma Malam Lawan kasan cewar mahaifin nasa mai Tsangaya ne, domin shi kansa ba zai iya tuna lokacin da ya fara karatu ba, kawai tashi yayi ya samu kansa yana karatu, amma ya fara fita Rani a shekara ta 2011, ya fara zuwa garin Gombe, Tsangayar Gwani Musa a unguwar
Fantami, da shekara ta dawo kuma sai ya zauna a Tsangayar Gwani Adam a Unguwar Arawa, daga nan bai kara zuwa ko ina karatu ba, duk abinda yayi a wajen
Mahaifin sa yayi...

Mahiru ya fara saukar sa ta farko ne a shekara ta 2014, lokacin bai fi shekara 18 ba. Wani abin mamaki; na daga cikin baiwar da Allah ya yiwa wannan babban alaramman shine: ya samu Tilawa tun a sauka ta farko (mun san mafi akasari ba kasafai mutum yake sauka da tilawa ba, sai wanda Allah yazaba) daga nan kuma sai ya kara sauka ta biyu lokacin tilawar sa ta kara karfi sosai kawai sai ya kama Satu.!

IJTIHADIN SA, DA JAJIRCEWAR SA WAJEN KARATU...

Gwani Allah yayi masa juriya da jajircewa a fagen karatu, domin a lokacin da yake neman karatu; ya kasance idan gari ya waye zai wanke allon sa yayi rubutu, yaje wajen Aramma (Mahaifin sa) yayi masa Darasu, sai ya tafi Iskali yai ta biyawa har zuwa Azahar, sannan sai ya dawo gida yayi Sallah yaci abinci, sai kuma yaci gaba da buga Allon sa a gida har zuwa sallar La'asar, idan akayi Sallah kuma, sai yazo gurin Darasu yana kallo baya yadda ayi Darasu baya kusa, kuma in dai akayiwa wani gyara, ko aka bashi wani harji wanda bai sani ba, a take yake kokarin haddace shi.

Sannan kuma karfe 03:00 na dare ya kanyi tashe zuwa Asuba, bayan Asuba ma yana kara biya Allon sa har zuwa karfe 7:00 na safe sannan ya wanke Allon sa. Kafin dai ya wanke yana biyawa kamar sau 313 ko sama da haka... TIRKASHI !

Gwani ya fara satu baifi shekara 18 ko 19 a duniya ba, kuma a saukar sa ta farko ana kamashi wajen darasu, amma duk inda aka gyara masa ya rikeshi kenan. 

YADDA YASAN HARJI DA LOGA:
Allah yabawa Gwani fahimta da kokarin bincike wajen sosai, ga kuma naci wajen yaga ya haddace Gegari, da yawa duk wanda zai haddace daukar carbi yake yai ta maimaita shi, sai ya biya kamar sau dubu ko sama da haka, kuma yana bibiyar rubu na kur'ani ya fitar da harjin da ke ciki wanda babu a wani rubun.

Gwani ya gamu da kalubale mai yawa a wajan neman karatu (Kamar yadda kowa yasan harkar karatu akwai matsaloli da suke riskar mutum kala-kala kamar rashin wurin kwana, da abinci, da tufafin sawa, da rashin kudin kashewa) duk da shi bai samu wata matsala ta rashin kudi ba, saboda lokaci-lokaci Mahaifin sa yana zuwa Gombe , in kuma yazo zasu hadu da shi ya bashi kudi yakai gurin Malamin sa ya ajiye, duk sanda ya bukata sai ya karba ya biya bukatar sa, amma ya dan samu matsalar gurin kwana a can Tsangayar Gwani Musa na unguwar Fantami lokacin babu masauki sosai, sai ya zamana suna kwana a cikin wani Garejin Mota, gasu da yawa sosai a ciki da masu fitsarin kwance, ko Mutum ba yayi kawai sai ya 
tashi yajishi cikin fitsari tsamo-tsamo wani yayi masa.!

Sai dai kash ! Allah ya jarrabi Gwani da wani babban iftila'i yayin da yake wannan gwagwarmaya, wanda shine babban kalubale da ya fuskanta. Abin ya faru ne kafin ya dawo daga Rani na karshe, ranar da zasu dawo gida Bojude sunje iskali sun dawo da safe, so akwai wani rami a kusa da iskalin nasu, so suna cikin kawai sai wasu yara suka tsokano wani mahaukaci, sai ya biyo su da gudu, su kuma suka shigo cikin Iskalin su, Jama'a suka fara guje-guje, so lokacin yana da dan laruri na ciwan kafa baya iya gudu sosai, ai kuwa yana fara gudu tsautsayi yasa yaje ya fada cikin wannan ramin. Kawai sai fito dashi akai ya karye a kafa.....

Sai aka dawo dashi gida a kayi jinyar sa, har ya warke ya fara tafiya da sanda ashe dorin bai yi ba, an yima sa gyara ya kai sau uku ba a dace ba, sai Mahaifin sa ya yanke shawarar fita dashi zuwa kasar waje domin a gyara masa kafar sa, ikon Allah Kenan ! ana cikin haka kawai sai Allah yayiwa Mahaifin nasa rasuwa.!!! 😭🙆🏼‍♂

Har yanzu maganar da ake sai ya dogara sanda yake tafiya.! Amma Gwani kullum cikin godewa Allah yake, saboda wannan jinyar bata hanashi karatu ba, a cikin wannan larurin ya hada tilawar sa, har yayi Satu, kai har ma ya rubuta Al-qur'ani, kuma ya taba wasu bangarori na Ilimi, kuma a halin yanzu shine yake jagorantar tsangayar Mahaifin sa, yanzu haka ma shine mai Darasu..

SANA'A DA KARATU:
Lokacin da Gwani yake zaman tsangaya duk da bashi da matsalar kudi, dama na sayan omone, kuma yana da shi, amma ganin yadda wasu yan uwa suke wasu sana'o'i haka yasa shima ya dan taba sana'ar dinkin takalmi a Lokacin.

Gwani ya rubuta Al-qur'ani sau daya, ya fara na biyu yanzu bai samu kammala wa ba saboda uzurai na rayuwa sai yayi sati biyu zuwa uku bai samu zama ba (zaku ga rubutun nasa mun saka a kasa).!

ILIMIN ADDINI DANA ZAMANI:
Gwani ya dan taba karatun Fiqhu, musamman Fiqhu na Malikiyya, ya karanta Ahlari, Ishmawi, Iziyyah da Risala. Ya kuma fara karatun bangaren Arabiyya kadan. Amma Bayyi karatun Boko ba, ya koyi Hausa da Turanci kadan agurin wasu abokan sa.

Gwani ba shi da Aure, (amma akwai kyakkyawan shiri) yana rayuwar sa cikin farin ciki da nishadi, baya bara ko maula, Arzikin Al-qur'ani duk abinda wani sa'an sa yake na rayuwa shima yana iyayi ko fiye da shima Alhamdulillah.

RUBUCE-RUBUCEN SA:
Yayi Rubuce-rubuce da suka shafi Harji, amma Allah baisa an wallafa ko daya ba.

ABOKAN KARATUN SA:
gwani yayi abokai sosai wadanda suka zauna suka amfani juna dasu sosai, daga cikin wanda bazai taba mantawa dasu ba akwai: Gwani Ashiru dan jihar Katsina, da Gwani Bakura dan jijar Gombe, da Gwani Khalid, da Gwani Ashiru Fikayal, suna dai da yawa duk tare suka zauna a Bojude, kusan tare sukayi Satu...

SHAWARAR SA GA 'YAN UWA ALMAJIRAI, DA MALAMAI:
Gwani ya bada shawara ga 'yan uwan sa Almajirai da dalibai akan su tsaya suyi karatu sosai tun suna da dama, don wallahi wataran ko suna so ba za su iya ba. 

Shawarar sa ga Gwayen da Alarammomi, dan Allah dan Annabi mu dinga yiwa junammu uzuri, mu daina yiwa juna kyashi da Hassada, wannan yana kawo ci baya sosai, kuma duk sanda kaga Allah yayiwa wani Almajiri sutura kayi murna kayi farin ciki, kaji tamkar kaine, tabbas in ka zama haka zaka ci riba a rayuwar ka ta duniya da lahira insha'Allah..

Daga karshe yana kira garemu baki daya; mu kara dagewa da addu'o'i, duk wanda yake son karya tsarin  karatun Al-qur'ani (Na Tsangayu)  Allah ya karya shi, ya lalata shirinsu, ya maida musu sharrin su kansu.(Ameen)

Muna rokon Ubangiji ya karama rayuwar gwanin nan namu albarka, ya haskaka rayuwar sa, ya jikan magabatan sa, ya yaukaka arzikin sa, ya kiyaye shi daga dukkan sharri, mu dashi baki daya.

Mai Gabatarwa: Yusuf Abdulkarim.

Wanda ya tattara:
Nuraddeen Umar Al-Husary (Autan Ƙolawa).

Wanda ya Sabunta:✍🏼
Salihu Mu'az Koki
Litinin 19/R/Sani/1441= 16/12/2019